JIRGIN ANSU FATI ZAI TASHI

Kungiyar kwallon kafa ta BRIGHTON na kasar Ingila ta cimma yarjejeniya da kungiyar kwallon kafa ta BARCLONA kan ɗan wasanta Ansu Fati

Dan wasan ƙwallon ƙafa ɗan asalin Saniya Ansu Fati dake taka leda a kungiyar kwallon kafa ta BARCLONA zai koma taka leda a kungiyar kwallon kafa ta BRIGHTON.

wannan yarjejeniya antabarne baya Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona tace Ansu Fati baya cikin yan kwallonta da zata sayar a wannan shekarar.

kungiyar kwallon kafa ta BRIGHTON ta amince kan daukar ɗan wasan gaba na Barcelona Ansu Fati amatsayin loan Wanda zai bugawa mata ƙwallo na tsawon shekara ɗaya 2024.

Tuni dai Ansu Fati yashirya kayansa domin tafiya kungiyar kwallon kafa ta BRIGHTON dake ƙasar Ingila.

Aranan Alhamis BRIGHTON zata karbi bakonci ɗan wasan aro Ansu Fati.

Rahoto: Fabrizio Romano.
Fassara: Adamu Ali usman

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started