Kodinetan jam’iyyar APC na jihar Borno ya fice daga jam’iyyar
Kodinetan kungiyar City Boys Progressive Group CBPG APC reshen jihar Borno ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar saboda wasu dalilai da suka wuce ikonsa.
Ko’odinetan CBPG Abubakar Ayuba ya bayyana cewa abin bakin ciki ne kuma abin takaici ne ga wannan gwamnatin da ta kasa magance matsalolin da suka addabi al’ummar kasar nan sakamakon tallafin man fetur da ke shafar tattalin arzikin Najeriya wanda ya jefa miliyoyin mutane cikin yunwa.
Ayuba ya kuma ce yana da kimar zaman sa tare da jam’iyyar All Progressive Congress APC da kuma damar da zai ba da gudummawar cimma burinsu baki daya, amma a yanzu ya yanke shawarar cewa ya yi ban kwana da APC domin ya zama dan Najeriya mai kishin kasa, fiye da ci gaba da kasancewa cikin wannan gwamnati da munanan manufofin.
Daga karshe, tsohon kodinetan CBPG APC reshen jihar Borno Abubakar Ayuba ya godewa jam’iyyar tare da gagarumin dama da gogewa.

