Abubuwan da Yakamata kusani gameda gasar cin kofin zakarun Turai ta shekarar 2023

Ayayinda kowani kasa ke dawowa da buga wasan ta na league na wannan shekarar 2023/2024 magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa ta duniya na fatan ganin anfara doka wasan cin kofin zakarun Turai.

kana dama na fatan sani dakuam jin ina matsayar haɗa wasan cin kofin zakarun Turai yake, musamman zagayen farko wadda ake haɗawa ga kungiyoyin kwallon 32 a kowacce shekara.

Wannan tsarin hukumar kwallon kafa ta yankin Turai ne ke tsarawa a kowacce shekara, ta hanyar zaɓo tsofaffin yan kwallon kafa domin ƙaddamar da wannan jadawalin wato (draws) a turance.

Wannan karon za’a kaddamar da jadawalin cin kofin zakarun Turai ne a ranan Alhamis 31 ga watan Ogosta shekarar dubu biyu da ashirin da uku 31/08/2023.

A cewar hukumar ta FIFA akwai yiwuwar canja tsare tsaren cin kofin zakarun Turai ta hanya karo wasu kungiyoyin kwallon kafa cikin tsarin domin saukawa kungiyoyin kwallon wajen cin kofin asawake.

Adamu Ali Usman

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started